Abun ba a cewakomi

ayan zuhaka ankayiwa niger hari kuma ba asan kosuwayeba a yanzude ananan anabinci ke akai
Za a hukunta waɗanda suka yi wa matan ƙauye fyaɗe bayan shekara 30

Babbar kotun jihar Tamil Nadu da ke Indiya ta tabbatar da hukuncin da aka yanke shekara 30 da suka wuce, inda aka samu ɗaruruwan jami’an gwamnati da laifin aikata miyagun laifuka, ciki har da yin fyaɗe ga wasu mata 18. Jami’an gwamnatin da aka samu da laifin sun haɗa da ƴan sanda da masu aiki a ɓangaren kula da gandun daji da kuma na tattara haraji. Jamai’an sun far wa wasu ƴan ƙauye a watan Yunin 1992, bisa zargin su da taimaka wa wani mai fasa-ƙwaurin itacen turare, mai suna Veerappan. Jami’an sun ci zarafin maza sannan suka yi wa mata fyaɗe, sun farfasa musu gidaje da halaka dabbobi da suka mallaka. An yi wa al’amarin laƙabi da ‘Shari’ar Vachathi’, wato sunan ƙauyen da aikata waɗannan laifuka. Dukkanin jami’ai 269 da aka zarga sun musanta aikata laifukan, sai dai a shekara 2011 wata kotu ta kama su da laifi a ƙarƙashin wata doka. An kuma samu mutum 17 daga cikin su da laifin aikata fyaɗe. Yayin da 54 daga cikin waɗanda ake zargin suka mutu a tsawon lokacin da ake shari’ar, an yanke wa sauran 215 hukuncin ɗauri da suka kama daga shekara ɗaya zuwa 10. Sai dai mutanen sun ɗauka ƙara a babbar kotun Madras da ke birnin Chennai a arewacin ƙasar. Lauyar waɗanda aka ci zarafin ta shaida wa BBC cewa an bayar da belin dukkanin waɗanda aka samu da laifin. Ta ce “Baya ga mutum 17 da aka kama da laifin fyaɗe, kusan dukkanin sauran ba su yi zaman kurkuku ba ko kaɗan.” A ranar Juma’a mai shari’a P Velmurugan ya umarci gwamnatin jihar ta biya kowace daga cikin waɗanda aka ci zarafi diyyar kuɗin rupee miliyan ɗaya, wato dalar Amurka 12,034 da kuma aikin yi. Hukuncin kotun ya kuma yi kira da a ɗauki mataƙi mai tsauri a kan shugaban ma’aikatan yankin na wancan lokacin, da babban malamin daji da kuma shugaban ƴan sandan yankin. A watan Maris, mai shari’a Velmurugan ya kai ziyara a ƙauyen na Vachathi, wanda ke kusa da tuddan Sitheri a gundumar Dharmapuri.

Comments

Popular posts from this blog

Sabun platform wandazakasamu kudisosai